17 Afirilu 2026 - 21:27
Source: ABNA24
Hizbullahi Ta Gudanar Ayyukan Ruwan Bama-Bamai 2184 Kan Isra'ila

Kungiyar Hizbullah ta jefa bama-bamai a yankunan da gudanar akan yankunan da Isra'ila ta mamaye cikin ayyukanta 2,184. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da wata sanarwa da ta bayyana cewa, dakarun gwagwarmayar Musulunci sun gudanar da hare-haren soji 2,184 a kan sojojin Isra'ila da Falasdinu da aka mamaye tsakanin 2 ga watan Maris zuwa 16 ga Afrilu, 2026. 

A cewar sanarwar, a cikin wannan lokacin. Hizbullahi a wannan dan tsakanin ta fitar da sanarwa a hukumance guda 1828 da ke bayyana cikakkun bayanai game da ayyukan da aka yi a kan sojojin sahyoniyawa a cikin Lebanon. Hizbullah ta kuma jaddada cewa, hadafofin wadannan ayyuka sun hada da wurare da barikoki da sansanonin sojin Isra'ila a yankunan Falasdinawa da suka mamaye. 

Sanarwar ta kara da cewa, mayakan kungiyar Hizbullah sun yi amfani da jirage marasa matuka na ƙunar baƙin wake da hare-haren makamai masu linzami iri-iri, inda suka kai hari ga birane da garuruwan Isra'ila daga kan iyakar Lebanon zuwa zurfin kilomita 160, da suka wuce har Tel Aviv. 

A cewar kungiyar, an kai hare-haren ne domin mayar da martani ga laifukan ta'addanci Isra'ila ta kai kan fararen hula tare da lalata kayayyakin more rayuwa na fararen hula a Lebanon. 

Sanarwar ta kuma ce, mayakan gwagwarmaya sun gudanar da ayyuka a matsakaicin adadi sau 49 a duk rana, kuma sun ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da fifikon bayanan sirri da karfin wutar "Isra'ila". 

A karshe dai kungiyar Hizbullah ta jaddada cewa har yanzu mayakanta suna da cikakken shiri kuma za su mayar da martani ga duk wani mataki na gwamnatin Sahayoniya.

Alkawarin da dakarun gwagwarmaya suka ɗauka ga shugabansu Sheikh Naeem Qaseem ga kuma al'umma masu daraja, masu 'yanci da sadaukarwa, shine su kiyaye alkawari har numfashin karshensu, kuma babu wata tuta da za ta fadi daga hannunsu".niya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha